A cewar rahoton Ofishin Yada Labaran Hauza, a ranakun farko na cika shekaru arba'in da bakwai (47) da nasarar juyin juya halin Musulunci da kuma fara bukukuwan "kwana goma na nasara" (Dahe Fajr), Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran, Ayatullah Sayyid Ali Khamene'i (Dz) da safiyar yau (Asabar 31 ga watan Janairu, 2026) ta ziyarci makwancin mu'assasin Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Imam Khomeini (Q), inda ya karanta addu'o'i gare shi tare da gaisuwar girmamawa.
Imam Khamenei, bayan ya karanta Fatiha da kuma yin salla a makwancin Imam Khomeini, ya yi addu'ar daukakar matsayi ga ruhin wannan babban Imam mujahidi, da kuma shuhadan juyin juya hali.



Your Comment